Wani likitan koda dake aiki a asibitin koyarwa dake Ikeja jihar Legas Theophillus Umeizudike yayi kira ga mata da su yawaita ziyartar asibiti akalla sau daya a shekara domin duba lafiyar su.
Ya fadi haka ranar Alhamis da yake hira da kamfanin dillancin labaran Najeriya a Legas inda ya bayyana cewa hakan zai taimaka wajen kare su daga kamuwa da cutar koda ganin cewa bincike ya nuna cewa mata sun fi kamuwa da cutar koda fiya fa maza a Najeriya.
” Bincike ya nuna cewa kashi 20 zuwa 30 bisa 100 na mata na yawan kamuwa da cutar koda.”
” Ana iya kamuwa da cutar koda idan hanyar da ita kodar take amfani da wajen fitar da dati a jiki ya toshe.”
Hanyoyin kamuwa da cutar koda ga mata kuwa sun hada da;
1. Hawan Jini.
2. Zubar/cire ciki.
3. Kamuwa da cutar ‘Fibroid’.
4. Cutar dajin dake kama mahaifa.
5. Kamuwa da cutar siga.