Sai an siyar da buhun shinkafa ‘yar gida kasa da naira 10,000 – Gwamna Bagudu

0

Gwamnan jihar Kebbi Abubakar Bagudu ya bayyana cewa gwamnatin jihar ta hada hannu da shirin samar da tallafi wa manoma na gwamnatin tarayya, ‘Anchor Borrowers Programme’ don ganin an siyar da buhun shinkafa ‘yar gida kasa da Naira 10,000.

Ya sanar da haka ne ranar Lahadi da yake amsar bakuntar ministan yada labarai Lai Mohammed a jihar Kebbi.

Bagudu ya ce shirin ‘Anchor Borrower Programme’ ya taimaka wa manoma da dama a jihar.

Ya kuma ce bayan masana’antun sarrafa shinkafa biyu da aka kafa (Labbana da Walcot) wasu kananan masana’antun sarrafa shinkafa a jihar sun sami dagowa.

A karshe Lai Mohammad ya jinjinawa gwamna Bagudu kan nasarorin da jihar ta samu wajen bunkasa aiyukan noma a jihar.

Share.

game da Author