RIKICIN MAMBILA: Mutane 20 ne suka rasa rayukan su, shanu sama da 300 aka sace

0

A jiya Lahadi ne wasu mazauna tsaunin Mambilla dake karamar hukumar Sadauna jihar Taraba suka bayyana wa PREMIUM TIMES cewa sanadiyyar rikicin da aka yi a tsaunin mutane 20 sun rasa rayukansu sannan an sace wa Fulani shanu 300.

A bayanin da ya yi wani mazaunin unguwan Leme dake kauyen Gembu mai suna Saadu Mogoggo ya ce ya rasa kannin sa biyu a rikicin sannan sun sace duk shanun da suke kiwo.

” Maharan sun kashe mahaifi na a watan jiya sannan suka sace shanun mu duka, sama da 100.”

” Ko da haka ya faru sai kannai na biyu suka kai karar harin wa sojoji ko dan saboda a gano shanun da aka sace, sai dai isan su ke da wuya inda maharan suke sai suka bude musu wuta nan take suka mut, shi sojan da ya raka su ya tsira da rauni a jikin sa.”

Shi kuwa Abdu Gagarau mazaunin kauyen cewa yayi kone-konen gidaje da kisan Fulani ya fara ne tun ranar Alhamis har zuwa safiyar ranar Lahadin makon da ya gabata.

Shugaban Fulanin na yankin, Ahmadu Nguroje a nashi tsokacin ya yi kira ne ga gwamnati da jami’an tsaro da su kawo musu dauki domin abin fa ya baci.

Nguroje ya ce bayan mutane 20 da aka kashe, an kona musu gidaje sannan an sace musu shanu sama da 200.

Bayan haka dan majalisan jihar wanda ke wakiltan mazabar Nguroje da Gembu Bashir Muhammed yace abin takaici ne yadda ake yi wa Fulani kisan gilla a tsaunin Mambilla duk da kokarin da gwamnati ke yi na ganin zaman lafiya ya kankama a yankin.

” Babu jam’an tsaro a wadannan wurare kwata-kwata saboda wuraren kauyuka ne wanda kan dauki mutum awoyii biyu ko fiye idan zaka je kauyukan, wanda hakan yakan zama sai yadda Allah yayi da mazauna yankin.”

Gwamnan jihar Darius Ishaku ya yi kira ga mutanen tsaunin Mambilla da su yi hakuri su zauna lafiya.

Ya kuma gargade su cewa laifi ne wani ya kashe dan uwan sa sannan duk wanda ya kashe wani a tsaunin Mambilla ko a duk fadin jihar za a hukunta shi kamar yanda ake hukunta masu aikata laifi.

Daga karshe kakakin rundunar ‘yan sandan jihar David Misal ya bayyana cewa tsakanin makiyaya da manoman yankin mutane 4 suka rasu daga kowani bangare.

Ya kuma ce sun aika da ma’aikatan su tsaunin Mambilla domin samar da zaman lafiya a tsaunin.

Share.

game da Author