Muna bukatan taimakon malamai akalla 6000 daga Najeriya – George Weah

0

Shugaban Kasar Liberiya, George Weah ya mika kokon barar sa ga shugaba Muhammadu Buhari da ya taimakawa kasar sa da malamai akalla 6000 domin bunkasa fannin ilimin kasar.

Weah ya bayyana haka ne da wadansu taimakon da yake bukata daga Najeriya a wani zantawar sirri da ya yi da shugaban Kasar Najeriya Muhammadu Buhari a fadar gwamnati dake Aso Rock, Abuja.

Bayan nan ya kara da cewa, kasar sa na bukatar taimako a fannin, kasuwanci da cinikayya, bankuna da ayyukan noma.

” Na ji ana ta rade-radin wai wasu bankunan Najeriya da ke aiki a kasar Liberiya na shirin rufe ofisoshin su na kasar. Ina rokon su da suyi hakuri, cewa wannan gwamnnati za ta bunkasa tattalin arzikin kasar liberiya ta yadda ba za su gudu ba.

” Najeriya kasa ce da ke da dimbin arziki kuma uwa ce ma ba da mama, muna rokon ta da ta sa mana hannu a fannin samar wa matasa aikin yi da bunkasa tattalin arziki ta hanyar kafa wasu kamfanoni a kasar mu.”

Wannan dai shine karo na farko da sabon shugaban kasar zai ziyarci Najeriya tun bayan rantsar da shi da akayi a watan Janairu.

Share.

game da Author