Wani gungun nakasassu sun gudanar da zanga-zangar lumana a Majalisar Tarayya jiya Talata.
Hasalallun dai sun gudanar da zanga-zangar ne a bisa dalilin su na rashin aikin yi.
Dukkan wadanda suka yi zanga-zangar dai sun yi ikirarin cewa duk sun cika fam na neman aiki a wurare daban-daban, amma an yi watsi da su.
Dalili kenan suka je Majalisar Tarayya a fusace su na kiran a daina nuna musu bambanci a wurin daukar ma’aikata don su na da wata nakasa a jikin su.
Har yau dai ba a sa wa Dokar Tilasta daukar nakasassu aiki ta 2016 ba. Amma kwanan baya Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki, ya ce tabbas an kusa gabatar da kudirin ga Shugaban Kasa domin ya sa mata hannu ya zama doka a cikin kwanaki 30.
Wani sashe na dokar wadda ake jiran a sa mata hannu, ya tanaji hukuncin naira milyan daya ga kamfani ko hukumar da ta nuna bambanci ko wariya ga nakasasshe a wurin daukar aiki.
Ta kuma tanaji tarar naira dubu dari, 100,000 ga mutumin da ya nuna wariya ga daukar nakasasshe ai. Akwai kuma zabi na daurin wata shida ga wanda ba ya iya biyan tara. Idan kuma abin ya hada izgilanci ga nakasasshe, to za a iya hada tarar da daurin a lokaci guda a matsayin hukunci.
Da ya ke magana da manema labarai, shugaban kungiyar nakasassun, Godstime Onyebulam, ya ce dukkan su sun kammala digiri a jami’o’i daban-daban.
Har zuwa lokacin rubuta wannan labari dai ba a kai ga saurarar su ba, amma jami’an tsaro sun rufe kofa, sun hana su shiga cikin harabar ginin majalisar.