Gabanin fara jarabawar share fagen shiga jami’a, UTME, wadda hukumar JAMB ke shiryawa , da za a fara a ranar Juma’a, 9 Ga Maris, 2018, Hukumar Shirya Jarabawar Shiga Jami’a ta Kasa, JAMB, ta na sake gargadin dalibai cewa kada su kuskura su shiga dakin jarabawa da kowane irin abin da aka haramta shiga da shi.
Cikin wata takarda da Babban Sakataren Hukumar, Ishaq Oloyede ya sa wa hannu, ya lisafa abubuwa 16 da suka hada da:
1) Agogo
2) Fensari ko biro
3) Wayar salula ko makamancin ta
4) Tabarau na kara lafiyar ido, sai an tabbatar da shi tukunna.
5) Kwakuleta ko raskwana
6) Na’urar boye bayanai kamar USB, CD da sauran su.
7) Littafin karatu ko na rubutu.
8) Kyamarar daukar hoto
9) Rikoda
10) Makirho
11) Maballin sauraren magana a kunne.
12) Tawwada da alkalami da makamantan su.
13) Tabaran hangen nesa
14) Zobe da sarkoki da ‘yan hannu
15) Maballi mai na’ura
16) Bluetooth.