Ya zuwa yanzu Najeriya ta shiga matsananciyar damuwa ganin yadda akasarin jihohin Najeriya suka ciwo bashin da ya yi musu katutu, kuma ya kumbura musu ciki, ya yi suntum, har cikunnan su ke neman fashewa.
Rahoton da Hukumar Kula da Yadda ake Kashe Kudade da Raba su, ta fitar da sabon rahoton da ya nuna cewa a daidai karshen 2016, akasarin jihohin Najeriya ana bin su bashin da ya zarce kashi 50 bisa 100 na kudaden shigar su na kowace shekara.
Jihohin Kudu maso Yamma ne abin ya fi shafa, domin biyar daga cikin su shida na daga cikin jihohi bakwai da bashi ya fi yi wa katutu.
Jihohi irin su Lagos, Osun, Cross River, kusan akwai nauyin bashi a kan su na kashi 480 kudaden shigar su, yayin da wasu jihohi 18 kuwa bashin su ya zarce samun kudin su da kashi 200.
Wannan bayani ya na cikin rahoton da Economic Confidential da ake bugawa a Abuja ta wallafa a yau Litinin.
Rahoton ya fallasa cewa wannan hanya na ciwowa da karbo basussuka da jihohi ke yi, ya kauce wa ka’idar Ofishin Kula da Basussuka, cewa bashin da ke wuyan kowace jiha, kada ya zarce kashi 50 bisa 100 na samun kudin shigar ta na watanni 12.
Haka dokar sashe na 222 zuwa na 28 na dokar zuwa jari ta 2007 ta gindaya.