Kungiyar JOHESU za ta fara yajin aiki a ranar 7 ga watan Afrilu

0

Kungiyar ma’aikatan kiwon lafiya JOHESU ta yi shelar cewa a ranar 7 ga watan Afrilu za ta fara yajin aikin ‘sai illa ma sha’Allahu.

Mataimakin kungiyar Chimele Ogbonna da ya sanar da haka ya ce shiga yajin aikin ya zama musu dole musamman yadda gwamnati ta yi kunen uwar shegu kan alkawuran da suka dauka musu da kuma biyan sauran bukatun su.

” Ba mu da ra’ayin shiga yajin aiki amma tun da duk hanyoyin da muka bi domin a sasanta da gwamnati kan biyan bukatun mu daga shekarun 2009 zuwa 2017 sun bai haifar da da mai ido ba dole za mu shiga yajin aiki.

Idan ba a manta ba a kwanakin baya ne kungiyar ta ba gwamnatin tarayya wa’adin kwanaki 30 daga ranar 5 ga watan Maris zuwa ranar 7 ga watan Afrilu 2017 domin ta biya mata bukatun ta cewa idan har wadannan kwanki suka karkare za su shiga yajin aiki.

Share.

game da Author