A raba aure na da mijina don ya amince wa wani ya kwanta da ni- Wata matan aure
Wata matan aure mai suna Musilimat Olasuyi ta kai karar mijin ta mai suna Oluwagbemiga a kotun Igando dake jihar Legas ta na neman a raba auren su da mijin ta saboda tilasta mata da yayi wai sai ta kwana da wani da ba muharramin ta ba.
Sannan kuma ta shaida wa kotu cewa mijin ta matsafi ne sannan ya na sace mata kaya, da kudin ajiyar ta a dakin su.
” Mijina ya sace min kudin ajiya na masallaci, sanna ya kwashe mini gwala-gwalai ya siyar. Ina rokon kotu da ta warware auren dake tsakani na da mijina.
Shi kuwa mijin Musilimat, Oluwagbemiga ya ce matar sa karya take yi cewa itace matsafiya wadda bata san darajar aure ba.
” Babu irin namijin da matata bata kwana da shiba a unguwan mu sannan don dibar albarka har kwana take yi da su a cikin gidan mu sannan a kan gadun mu na sunna.
Alkali Akin Akinniyi ya yanken hukuncin cewa kotu za ta ci gaba da shari’ar ranar 26 ga watan Afrilu.
Discussion about this post