Wasu magoya bayan jam’iyyar PDP su ‘4000’ a karamar hukumar Birnin Kudu, sun kunyata Gwamna Abubakar Badaru na Jihar Jigawa, yayin da aka neme su ko sama ko kasa domin Gwamnan ya yi musu wanka komawa APC, amma aka rasa.
Gwamna Badaru ya je Birnin Kudu ne a jiya Lahadi, inda ya yi niyyar karbar wadanda su ka canja shekar da kuma kaddamar da ayyukan raya al’umma.
Danmajalisa mai wakiltar Birnin Kudu da Buji, Magaji Da’u Aliyu ne ya shirya taron, tare da bayar da gudummawar motoci ga magoya baya. An kuma kaddamar da aikin gina titin birji, kuma aka bada takardar cakin kudi na naira miliyan 20 ga daliban karamar hukumar da ke karatu a makarantun gaba da sakandare.
Yayin da aka kira wanda zai yi jawabi a madadin wadanda suka yi canjin shekar domin ya karanta jawabin sa, amma aka rasa shi, babu shi kuma babu sauran mutane ‘4000’ da aka ce su na tare da shi.
Wannan abu bai yi wa gwamna dadi ba, inda ya gaggauta gabatar da na sa jawabi a takaice ya bar wurin.
Shugaban taro Danmajalisa Da’u Aliyu bai yi wa manema labarai jawabin komai ba.