SANKARAU: Mutane takwas sun rasu a jihar Katsina

0

Jami’in yada labarai na karamar hukumar Jibia jihar Katsina Saadu Suleiman ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa mutane takwas sun rasa rayukan su sanadiyyar kamuwa da cutar sankarau.

Suleiman ya ce maza biyar da mata uku ne suka rasu sannan a tsakanin ranakun Litini zuwa Juma’a.

Kwamishinan kiwon lafiya na jihar Mariatu Usman da take tabbatar da haka wa gidan jaridar ta ce an fara samun labarin bullowar cutar ne a kauyen Bugaje dake karamar hukumar Jibia ranar 17 ga watan Janairu.

” A yanzu haka muna zaton mutane 22 ne suka kamu da cutar a wannan karamar hukumar wanda hakan ya sa muka zage damtse wajen gudanar da bincike, bada magunguna da wayar da kan mutane game da hanyoyin da za su bi don gujewa guje wa kamuwa da cutar.”

A karshe Mariatu ta ce za su fara yin allurar rigakafin cutar a garuruwan Bugaje da Gangara dake karamar hukumar Jibia da duk inda aka yi fama da cutar.

Share.

game da Author