WAEC ta canza ranar rubuta jarabawar da ta sa daidai lokacin sallar Juma’a

0

Hukumar shirya jarabawar kammala makarantar sakandare WAEC ta canza ranar rubuta jarabawar Chemistry da ta saka ranar Juma’ah kuma daidai lokacin Sallah.

Wannan jarabawa dai an mai da shi zuwa ranar Talata maimakon Juma’ah.

Idan ba a manta ba Musulmin kasar nan sun soki lamirin Hukumar Shirya Jarabawar kammala Sakandare (WAEC) kan yadda ta shirya za a rubuta jarabawar Chemistry a daidai lokacin sallar Juma’a.

A cikin tantebur din jarabawar Mayu/Yuni 2018, an tsara daliban da za su rubuta jarabawar Chemistry cewa za su fara jarabawar ne da karfe 2 – zuwa 5 na yamma, a ranar 20 Ga Afrilu.

Shugaban Kungiyar Kare Hakkin Musulmi ta Najeriya, Ishaq Akinbola ya bayanna jadawalin jarabawar da cewa bai yi wa musulmi adalci ba.

Ya kuma kara cewa hakan na yin nuni da yadda ake tauye wa musulmi hakki da ‘yancin su a kasar nan.

“ Matsawar aka ce babu adalci, to zaman lafiya ba zai taba samuwa ba. Shi ya sa kowa ke ta hankoron a samu wanzar da zaman lafiya.”

Share.

game da Author