Kotun Daukaka Kara ta Abuja a jiya yau Juma’a ne ta yi watsi da karar da Sanata Dino Meyaye ya daukaka a gaban ta, inda ya kalubalanci kiranyen da INEC za ta shirya yi masa a mazabar sa.
Alkalai uku ne suka zauna sauraron karar a zaman karshe, kuma duk suka yi watsi da karar, inda su ka yanke hukuncinn cewa INEC nac da damar da za ta shirya masa kiranyen, kamar dai yadda babbar kotun tarayya ta yanke tunda farko.
Masu shari’ar sun bayyana cewa kwanaki 90 da doka ta bayar cewa a gudanar da kiranyen daga ranar da aka nemi a yi, ai bas u shige ba. Tsaiko ne aka samu daga ranar 6 Ga Yuli, 2017, a lokacin da Mai Shari’a Dantsoho ya dakatar da shirin yi masa kiranye tun daga ranar 23 Ga Yuni, 2017.
Dama tun da farko sai da Mai Shari’a Dimgba Nnambi na Kotun Tarayya ya fara korar karar da Dino ya shigar. Amma sai alkalin ya gindaya matakan da sai an cika su sannan za a yi masa kiranye.
Alkali y ace sai an aika wa Dino kwafen takardun jama’ar da ke son yi masa kiranye tare da sa hannun kowanen su. Daga sai Dino ya daukaka kara.
Sai dai kuma alkalan Kotun Daukaka Kara karkashin jagorancin Mai Shari’a Tunde Awotoye, sun jadda hukuncin da Dimgba ya zartas, har su ka kara da cewa bai kamata ma Kotun Tarayya din ta tsaya ta saurari kararv ba.
Awotoye ya kara da cewa zargin da Dino ya yi cewa INEC ba ta yi masa adalci ba, ba gaskiya ba ne.
Daga nan sai kotu ta ce ai dokar kasa ce ta bai wa INEC ‘yancinn yi wa wakilin jama’a kiranye, matsawar wadanda suka tura shi wakilcin sun nemi a yi hakan. Don haka babu wata kotun da ta isa ta dakatar da INEC.
Discussion about this post