BUHARI: Mantuwa ya ke dashi ne, ko Sakaci, ko kuwa Rashin Sani ne?

0

Shugaba Muhammadu Buhari na cikin halin fama da matsin-lamba a fadin kasar nan. Wannan kuwa ya danganta ne da irin salon mulkin da ya ke gudanarwa, wanda jama’a da dama ke ganin cewa shugaban ya yi musu bazata, wato ba haka su ka yi tsammanin zai kasance idan ya hau mulki ba.

Duk da wannan matsin-lamba da ya ke sha dalilin kura-kuran da ya ke tafkawa, mabiyan sa ko masoyan sa da yawa har yanzu ba su yadda ya na kuskure ba. Idan ma sun yarda din, su kan tirje su ce ‘ai dai gara Buhari da Jonathan.’

Wadanne kura-kurai ne Buhari ke tafkawa? Me ya sa wasu ba su yarda ya yi kuskure, ko da kuwa shi da kan sa ya gano kuskuren ya yi? PREMIUM TIMES HAUSA ta yi nazarin wasu muhimmman batutuwa domin ku buga lissafi a kai.

HARKALLAR BABACHIR: Lokacin da Majalisar Dattawa ta taso Babachir Lawal, tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya a gaba cewa an kama shi da laifin harkallar kwangilar noman ciyawa a kogin Yobe. Da farko Buhari bai yarda ba. An gabatar masa da hujjoji, sannan kuma ya nemi ya cire shi kafin a kammala bincike. Buhari bai yi haka ba, maimakon ya damka binciken ga EFCC, sai ma ya nada kwamiti da kan sa, daga baya kuma ya ce wa Majalisar Dattawa ai Babachir Lawal ba shi da laifi.

Sai da aka dauki tsawon lokaci ana tataburza da Buhari, sannan ya dakatar da shi. Kuma har yau ba a gurfanar da shi a gaban alkali ba.

AUREN DIYAR GANDUJE: Buhari ya sha suka da caccaka sanadiyya halartar daurin auren ’yar gidan Gwamna Abdullahi Ganduje na Kano da dan Gwamna Ajimobi na Oyo. Ya halarci daurin auren kwanaki kadan bayan Boko Haram sun sace dalibai mata sama 100 a sakandaren garin Dapchi a jihar Yobe. Sannan kuma ana tsakiyar jimamin kashe-kashen gilla da aka yi wa jama’a, akasari talakawa a jihohin Zamfara, Benuwai, Adamawa da Taraba. (Premium Times Hausa) Kuma duk babu wanda ya je yi musu jaje ko ta’aziyya. Wannan ya jawo masa kakkausar suka musamman ga talakawa su na cewa ashe maganar kishin talakan da Buhari ke ikirari ma duk a baki ne kawai. Wasu kuma na cewa yanzu giyar mulki ce ya ke sha ya yi tatil, shi ya sa ya fi maida hankali ga sha’anin bukukuwan masu mulki, bai damu da talakawa ba. Sai da aka nemi hana shi barci mai nauyi saboda caccaka, sannan ya fara zuwa jaje da ta’aziyya.

HAUSAWA NA CEWA,: Hausawa na cewa, ‘‘fara koyon mulki da baki, kafin ka fara koyon mulki da hannu.’’ Buhari na shan suka wajen yin kasassaba ko katobara ko kuma subul-da-baka. A ziyarar da ya kai jihar Taraba, ya bayyana wa gwamnan jiyar Darious da manyan kasar cewa shi duk abin da ke faruwa a kasar nan, ya na da hanyoyin da ya ke samun cikakken bayani. (Premium Times Hausa) Wannan ma ya bai wa jama’a mamaki, domin a cewar su, to me ya sa ba ya saurin daukar matakai kenan?

JANGWANGWAMAR ABDULRASHIR MAINA: A daya bangaren kuma Buhari na saurin furta rashin sanin sa da abubuwan da ke faruwa a kasa duk da irin muhimmancin su. Har aka maida Abdulrashid Maina a cikin gwamnatin tarayya a matsayin darakta, Buhari bai sani ba. Sai daga baya ya yi ta kame-kamen bayar da umarni a yi binciken dalilin maida tsohon shugaban hukumar fanshon ma’aikata a cikin gwamnati. (Premium Times Hausa) Har yanzu kuma ministoci da manyan ma’aikatan da ke da hannu kan asarkalar dawo da maina, babu abin da aka yi musu.

KWATAGWALCIN SUFETO JANAR IDRIS: Wannan al’amari zai dade a zukatan ‘yan Najeriya, jin Shugaba Buhari ya furta da bakin sa cewa ya bai wa Sufeto Janar Idris Ibrahim umarnin ya koma jihar Benuwai ya tare can har sai zaman lafiya ya wanzu, an daina rikicin makiyaya da manoma, amma ya bijire bai je ba. ’Yan Najeriya sun rika yi wa kan su tambayoyi sama 100. (Premium Times Hausa) Shin me ya sa mukarraban Buhari suka raina shi ne? Wane irin shugaban kasa ne zai bai wa shugaban ’yan sanda umarni, amma dai bayan wata biyu ya fito ya ce ai bai ma san ba a bi umarnin da ya bayar ba?

JAR DARDUMA A DAPCHI: Buhari ya sha suka har daga wasu ‘yan jam’iyyar APC, irin su Shehu Sani, wdanda suka cika da mamakin don me za a shimfida masa jar darduma a Yobe, shi da ya je jajen sace ‘yan mata sama da 100 a makarantar Dapchi. Shin idan mukarraban sa ba su san abin da ya dace ba, shi ma bai sani ba ne? Wannan ya sa mutane irin su Shehu Sani bayyana wa duniya cewa, “ana shimfida wa manyan baki jar darduma su taka a bukukuwan ‘yan kwalisa ne, ba a wurin jaje da alhini a Dapchi ba.

COGE A KASAFIN KUDI: Lokacin da Goguwar Kasafin 2016 ta tirnike, Buhari ya ce shi bai ma san wata kalma wai ita ‘asarkalar kasafin kudi’ wato ‘budget padding’ ba.

SAKWARKWACEWAR ASIBITIN FADAR SA: Babu wanda ya san mummunan halin da asibitin cikin Fadar Shugaban Kasa ke ciki, har sai lokacin da uwargidan sa Aisha Buhari ta je, domin a duba lafiyar ta. Abin takaici da same asibitin ko sirinji babu. Wannan al’amari ya bai wa jama’a mamaki cewa hatta abin da ke kusa da Shugaban Kasa ma bai san halin da ya ke ciki ba.

‘BAKI SHI KE YANKA WUYA’: Wannan ma wata karin magana ce da Bahaushe ke yi, kuma ta yi daidai da wani furuci da Buhari ya yi kwanan nan, wanda talakawa ke ta tsangwamar sa. (Premium Times Hausa) “Ina jin farin ciki a zuciya ta, idan na ga matasa a cikin kartsetsiyar rana sun yi gumi, su na neman na kan su. ” Wannan kalamai sun bai wa matasa haushi sosai, kuma a halin yanzu su ne ake ta watsawa a soshiyal midiya ana caccakar Buhari cewa shi dama ba shi da wani tsari na samar wa matashi sukunin rayuwa, sai ya kare rayuwar sa a cikin rana sannan zai samu abinci?

AN GAMA DA BOKO HARAM: Akwai manya da kananan kura-kurai da a ke tafiya ana tafkawa. Wadanda abin ya dama su na korafi. Wadanda ba su so a ce ya yi laifi kuwa ba su ganin laifi ko kuskuren sa. Daga cikin wadannan akwai yawan furta cewa an gama da Boko Haram da ya rika yi can baya, ba sau daya ko sau biyu ba. (Premium Times Hausa) Amma tun da Boko Haram suka sace daliban Dapchi sama da 100, bai sake buda baki ya ce an gama da Boko Haram ba. Dama kuma masu jin haushin wannan kalamai daga bakin sa kan rika cewa, “to idan an gama da Boko Haram, ina daliban Chibok da ke hannun su tun cikin 2014?”

Share.

game da Author