Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufa’I ya aza tubulin ginin gidaje 600 da babbar kantin siyar da kayayyakin masarufi a jihar Kaduna.
An yi bukin aza harsashin ginin ne a unguwar sabon Kaduna da ake kira ‘Millennium City’.
Kamfanoni masu zaman kan su ne za su yi wannan aiki tare da hadin guiwar Hukumar saka Jari ta jihar Kaduna.
El-Rufai ya ce gwamnati za ta samar da ruwan sha, tituna, wutan lantarki da tsaro ne kawai, in da su kuma kamfanonin za su gina gidajen.
Bayan haka za a kammala gina katafaren kantin masarufi a wannan rukunin gidaje da za agina nan da watan Yuni.