Bakin cikin sace ‘ya’yan mu ba zai sake mu ba idan ba dawo da Leah aka yi ba- Mazaunan #Dapchi

0

A ganawar da mazaunan kauyen #Dapchi dake jihar Yobe suka yi da PREMIUM TIMES a garin #Dapchi sun bayyana mana cewa bakin cikin sace ‘ya’yan su da Boko Haram suka yi ba zai rabu da su ba muddun ba dawo da Leah Sharubu aka yi ba.

Idan ba a manta ba a watan Faburairu ne Boko Haram suka sace ‘yan mata 110 a makarantar sakandare dake Dapchi.

Ita Leah bata samu dawowa cikin wadanda aka dawo da su bane don ta ce ita ba za ta musulunta a can ba sannan ba za ta saka hijabi ba.

Boko Haram sun bata zabi da ta amince da hakan ko su bar ta tare da su.

Dori Kadau, wani mai fada aji a kauyen Dapchi ya shaida mana cewa tabbas suna cikin juyayi da damuwa duk da an dawo musu da ‘ya’yan su amma Leah da bata dawo da sauran ba shine ke ci musu tuwo a kwarya.

Kadau ya ce suna kira ga shugaban kwamitin dawowa da ‘yan makarantan Bashir Manzo da ya isar da sakon su ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya matsan gaske domin ganin an ceto Leah.

Ya kuma ce suna kira ga Boko Haram ta gidajen jaridu da su tsausaya musu musamman iyayen wannan yarinya su dawo da ita.

Share.

game da Author