Gwamnatin Neja ta biya wa daliban jihar kudin jarabawar WAEC

0

Gwamnatin jihar Neja ta biya Naira miliyan 300 wa daliban da za su rubuta jarabawar kammala makarantar sakandare WAEC a bana.

Kwamishinan ilimin jihar Fatima Madugu ce ta sanar da haka wa manema labarai inda ta bayyana cewa gwamnan jihar Abubakar Bello ya amince da haka ne a taron kwamitin zartarwa na jihar.

” Gwamnatin Abubakar ta gaji bashin kudaden hukumar WAEC sama da naira miliyan 950, sun samu daidaituwa tsakanin Hukumar da gwamnati game da yadda zasu biya bashin a hankali a hankali.

Bayan haka kwamishinan ruwa Mamman Musa ya ce gwamanti ta ware Naira miliyan 700 domin samar da ruwan sha wa mutanen jihar.

Ya ce za a yi amfani da wannan kudade ne wajen siyo kayan aikin samar da ruwa domin garuruwan da suka hada da Minna, Bida, Suleja, Kontagora da sabon Bussa.

A karshe kwamishinan shari’a Nasara Dan-Malan yace gwamnati ta amince da kudirin kafa cibiyar tattance kwararun malamai a jihar.

Ya ce nan ba da dadewa ba za a mika kudirin ga majalisar dokokin jihar.

Share.

game da Author