Daya daga cikin mutanen da ke fuskantar shari’a a gaban alkali dangane da harkallar shigo da dimbin bindigogi har 661 a kasar nan, ya bayyana wa mai shari’a a kotun tarayya cewa naira miliyan daya ya raba wa jami’an tsaro su ka bude masa kofar arcewa da muggan makamai daga tashar jiragen ruwa ta Lagos.
Mataimakin Kwanturola na Kwastan, mai suna Mamood Hassan ne ya bayyana haka a lokacin da jami’an bincike na SSS ke masa tambaya kuma su na daukar jawabin nasa a rikoda.
An gabatar da wannan murya tasa a gaban alkali Adetunde Faji, da ke Babbar Kotun Tarayya ta Lagos a jiya Litinin.
An gurfanar da Hassan da wani jami’in kwastan mai suna Salisu Danjuma da kuma wasu mutane uku, Oskar Okafor, Donatus Achinulo da Mathew Okoye, ana tuhumar su da laifin shigo da muggan makamai, yi wa kasa makarkashiya, yin fojaren takardun bayanai da kuma baiwa jami’an gwamnati toshiyar baki.
Cikin watan jiya ne lauyan Hassan mai suna Yakubu Galadima, ya kalubalanci mika rikodin din muryar Hassan a gaban kotu, ya na mai cewa an dauki muryar bayanin da ya yi ne bayan an tirsasa shi ya yi magana.
Daga nan sai lauyan nasa da wasu lauloyi suka nemi a yi bincike a cikin shari’ar domin a hakkake shin a cikin hayyacin sa ya yi maganar ko kuwa tilasta shi aka yi ba da son ran sa ba.
Wannan ne ya sa a makon da ya gabata aka daga shari’ar zuwa jiya Litinin kenen.
An dai dauki rikodin na bidiyon bayanain da jami’in kwastan Hassan ya yi a ranar 27 Ga Maris, 2017, inda aka nuno shi ya na bayanin cewa:
“Na raba wa jami’an tsaro naira milyan daya amma ba domin su kauda kai na fice da kwantinar bindigogin daga tashar jiragen ruwa ba.
” Na ba masu duba kayan da aka shigo da su naira dubu 200,000, CIO naira dubu 100,000, sai wasu masu biciken na ba su naira dubu 200,000, ‘yan sanda na raba musu naira dubu 200,000. SSS kuma tsakanin naira dubu 20,000 zuwa dubu 30,000. Na raba naira dubu 20,000 a bakin kofar fita, sai kuma naira dubu 50, 000 a kofar fita ta karshe.”
Hassan yace da farko dai naira miliyan 3.8 suka tsadance da mai kwantinar zai biya shi kuma zai fitar masa da kwantinar wadda ya ce karafuna ne a ciki.
Har ila yau dai a cikin bidiyon da ake yi masa tambayoyi wanda aka gabatar a gaban kotu, Hassan ya ce amma da ya gano cewa bindigogi ne har 661, a cikin kwantinar, sai ya ce sai an biya shi naira milyan 4.
Baya ga fojaren takardun shigo da kayan da aka yi, an kuma ji yadda Hassan ya bai wa wani babban jami’in kwastan mai suna Aliyu Musa naira dubu 400,000, don kada ya binciki abin da ke cikin kwantinar mai lamba PONU 825914/3, wadda aka dankare ta da makamai.
An kuma gano cewa ta hannun wani abokin aikin sa mai suna Danjuma Abdullahi ne ya bai wa wasu jami’an gwamnati a tashar ruwa ta Apapa har tsabar kudi naira miliyan daya.