Akwai wasu gidajen nawa, El-Rufai yaje ya rusa – Suleiman Hunkuyi

0

Sanata mai wakiltan Kaduna ta Arewa, Suleiman Hunkuyi ya bayyana cewa ba shi wani dalilin da zai sa yaki yafe wa El-Rufai don ya rusa masa gida.

” Na yafe wa El-Rufai, don a wurina dan uwa ne. Babu komai.”

” Don ya rusa mini gida banga dalilin da zai sa wannan abu ya hanani barci ba. Tambayar da nake yi kan rusa gida na shine me ya kai sojoji wannan gida da karfe 4 na asuba.

” Ina fata wannan abu da akayi mini ya zama zakka ce ga siyasa da ‘yan siyasan Kaduna da El-Rufai ya ke muzgunawa. Ba wani abu bane dan na yi wa siyasa irin wannan hidima.

Abin da nake so ku sani shine wannan ofis da shine El-Rufai ya fara balaguron kamfen din sa tun kafin ya zama gwamna. Sannan kuma idan El-Rufai yana ganin hakan ne ya zaba salon siyasar sa, ya sani gidan da nake zama yana lamba 18, titin Inuwa Wada dake Kaduna, zai iya zuwa ya rusa nan ma.

” Bayan haka ina so in tuna wa El-Rufai cewa ina da wani gidan a titin Queen Elizabeth, dake Zaria, inda har kwana ya sha yi lokacin da muke nema masa mutane su zabe sa. Ita ya je ya rusa.

Share.

game da Author