Wasu ‘yan bindiga sun kai hari makarantar mata a Yobe

0

A daren Litini da misalin karfe 7 na yamma wasu ‘yan bindiga da ake zaton ‘yan Boko Haram ne suka kai hari garin Dapchi dake karamar hukumar Damaturu a jihar Yobe.

Mazauna kauyen wanda mafi yawan su daliban kwalejin Damaturu ne sun arce ciki daji jin harbe- harbe da kone- konen gidaje da wadannan mutanen suke yi.

Wani mazaunin kauyen ya ce ya tsira da ran sa ne bayan ya arcewa cikin kungurmin daji sai dai kuma bai sani ko sun yi garkuwa da wasu ba.

Bayan haka kwamishinan ‘yan sanda jihar Abdulmaliki Sunmonu ya bayyana cewa maharan sun sace kayan abinci a kwalejin matan sannan sun yi garkuwa da wasu maza uku.

ya ce ba shi da masaniyyar ko wadannan mutane sun yi garkuwa da wasu amma sun tura jami’an tsaro kauye.

Share.

game da Author