Mutane 18 sun rasa rayukan su a rikicin Zamfara

0

Rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara ta bayyana cewa wata sabuwan rikici ta sake barkewa a kauyen Birane dake karamar hukumar Zurmi ya yi sanadiyyar rayukan mutane 18.

Kakakin rundunar Muhammad Shehu ya sanar da haka wa manema labarai ranar Alhamis in da ya ce mutane 18 sun rasa rayukansu a rikicin.

Rikicin ya kaure ne tsakanin wasu ‘yan farauta da wasu mutane a dajin Birane da suke zargin barayin shanu ne.

Masu farautan sun kama wani mutumi ne da suke zarge sa da satan shanu, inda bayan sun nemi yayi musu bayani kan inda ya samu wannan shanu da yawa sai arce da gudu.

” Ko da mutumin ya gudu ashe ya tattaro ‘yan uwan sa ne dake karamar hukumar Isah a jihar Sokoto inda aka yi kare jini biri jini a wannan daji washe gari.”

Shehu ya ce ko da suka iso dajin gawar mazaunan kauyen Birani ne kawai suka tadda sai dai ma’aikatan su za su tabbatar sun kamo duk wanda yake da hannu a wannan harin.

Share.

game da Author