Kwanaki uku bayan da aka yi wa al’ummar jihar Zamfara kisan-gillar mutane 41, gwamna Abdul’aziz Yari yayi zaman sa a Abuja bai ko leka gida ba.
Yari dai shi ne Shugaban kungiyar Gwamnonin Najeriya, kuma har zuwa yau Juma’a bai kai ga lekawa jihar ba.
Wasu maharan da ake zargi barayin shanu ne, su ka kai wa kauyen Birane hari, kuma suka kashe mutanen. Birane na cikin karamar hukumar Zurmi.
Kakakin Rundunar ‘Yan sandan jihar Zamfara, Mohammed Shehu, ya ce tun da farko, wasu ‘yan farauta ne daga kauyen Birane su ka bi sawun wani barawon shanu a daji.
Ya ce sun same shi da shanu da tumaki, amma sai suka yi sakacin da ya arce. Bayan ya gudu ne sai ya tsallaka cikin Karamar Hukumar Isa, da ke jihar Sokoto, ya dawo tare da zugar makasa kan babura masu yawa.
Jaridar Vanguard ta ruwaito wani ganau ya ce makasan a kan Babura su ka yi wa kauyen dirar-mikiya, inda ba su yi wata-wata ba, sai suka bude wuta har suka kashe mutane 41.
Silar rikicin ya faro ne bayan rikicin ya kaure ne tsakanin wasu ‘yan farauta da wasu mutane a dajin Birane da suka zarga barayin shanu ne.
Masu farautan sun kama wani mutumi ne da suke zarge sa da satan shanu, inda bayan sun nemi yayi musu bayani kan inda ya samu wannan shanu da yawa sai arce da gudu.
” Ko da mutumin ya gudu ashe ya tattaro ‘yan uwan sa ne dake karamar hukumar Isah a jihar Sokoto inda aka yi kare jini biri jini a wannan daji washe gari.”
Shehu ya ce ko da suka iso dajin gawar mazaunan kauyen Birani ne kawai suka tadda sai dai ma’aikatan su za su tabbatar sun kamo duk wanda yake da hannu a wannan harin.
Wani dan jarida da ke zaune a jihar Zamfara ya ce makasan sun sake komawa kauyen a ranar Alhamis, inda suka kara kashe mutane da dama.
“Ina tabbatar muku cewa a yanzu wadanda aka kashe a cikin kwanaki biyu a hauyen, sun kai mutane 74.
Kwamishinan Yada Labarai Sanda Danjari ma bai san an kai harin ba, har sai ranar Alhamis da ya ce ya ji labarin a Sashen Hausa na Gidan Radiyon France.
Ya ci gaba da cewa ya yi kokarin ya sanar da gwamnan ta wayar tarho, amma ya kasa samun sa.
Majiya ta ce hanyar shiga kauyen Birane ta na hadari sosai kuma ba ta da kyau.
Discussion about this post