Ladar naira miliyan uku ga duk wanda ya tsegunta maboyar Shekau

0

Hukumar Tsaro ta Sojojin Najeriya, ta yi alkawarin bayar da ladar naira miliyan uku, ga duk wanda ya tsegunta mata mabuyar shugaban Boko Haram, Abubakar Shekau.

Kakakin yada labaran sojojin, Sani Usman ne ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya fitar. Wannan ne dai karo na uku da aka sa ladar tsabar kudi ga wanda ya tona inda Shekau ya ke. Daga 2012 ne aka fara aza ladar, amma har yau babu wanda ya fito ya bayyana shi.

Cikin watan Nuwamba, 2012, gwamnatin tarayya ta bayyana cewa duk wanda ya tsegunta inda Shekau ya ke, to zai samu lada ta naira miliyan 290.

Sai kuma cikin Yuni, 2013, nan kuma Amurka ce ta bayyana albshir na ladar dala milyan bakwai ga duk wanda ya labarta inda Shekau ya ke.

A bisa dukkan alamu, darajar Shekau ta ragu kenan, ganin yadda ake rage masa farashi, watakila domin la’akari da sojoji ke yi cewa sun kakkafe Boko Haram, sai dan burbushi ya rage.

Sau da dama dai rundunar sojoji ta sha cewa ta kashe Shekau, amma daga baya sai a gay a fito a cikin sabon bidiyo ya na kalubantar masu cewa an kashe shi.

Share.

game da Author