Mijina na yi mini barazanar sai ya kashe ni – Wata Matan Aure

0

Wata mata mai suna Eunice ta maka mijin ta a kotun dake Igando jihar Legas saboda yawan barazanar kashe ta da yake yi.

Eunice ta bayana cewa ta auri mijinta mai suna Enebeli shekaru 16 da suka wuce sannan sun haifi yara uku bayan auren (namiji daya da mata biyu masu shekaru 10,13 da 15).

Ta ce ta fara samun matsala da mijinta Enebeli a watan Fabrilu 2017 bayan kaurace mata da ya yi matsayin ta na matarsa.

” Bai tsaya a kaurace mini ba Enebeli ya tattara kayan sa ya fice daga gidan da muke zama tun a watan Agustan 2017″.

Eunice ta ce dawowar sa ke da wuya sai ya fara yi mata barazarar sai ya kashe ta sannan kuma ya ce zai sace dan su namiji ya ware da shi.

Shi kuwa Enebeli ya ce kazafi ne kawai matarsa take yi masa domin ko da wasa bai taba yin barazanar dauke ran matar sa ba ballanta na kuma ya sace dan da ya haifa.

Enebeli ya yarda da kotu ta warware auren dake tsakanin su.

Alkakin kotun Akin Akinniyi ya yanke hukuncin warware auren sannan ‘ya’yan su uku su ci gaba da zama da mahaifiyar su sannan mahaifin su zai ci gaba da biya musu kudin makaranta kuma zai kawo Naira 15,000 duk wata kudin abincin ‘ya’yan.

Share.

game da Author