Za a kafa sansanin Rundunar Sojojin Sama a Jihar Taraba

0

Hafsan Hafsoshin Sojojin Sama, Sadique Abubakr, ya bayyana shirye-shiryen da ake a kai wanda hukumar sojojinn saman kasar nan za ta kafa sansani a jihar Taraba.

Ya bayyana cewa za a kafa sansanin ne domin kawo karshen fadace-fadacen da ake yawan yi tsakanin makiyaya da kuma manoma a cikin kasar nan.

Abubakar ya bayyana haka ne a yayin da ya ke gabatar da wata lacca a Kalejin Dabarun Tsaron Kasa, a Abuja a ranar Alhamis.

Ya kara da cewa baya ga wannan za a kafa wani sansani na zaratan kai daukin gaggawa a tsakanin Jihohin Benuwai da Nassarawa.

Share.

game da Author