Mataimakin Shugaban Kasa Yemi Osinbajo, ya amince da cewa kafa ‘yan sandan jihohi shi ne mafita wajen magance matsalar tsaro a kasar nan.
Ya ce kowane dan Najeriya na da ‘yancin samun cikakken tsaro daga gwamnati, kuma ba da gangar ba ne da gwamnati ta kasa magance tsaro a wannan lokaci.
Ya yi wannan jawabi a wurin Taron Gano Makamar Tsaro na Kasa da Majalisar Tarayya ta shirya.
“Ba za mu iya kula da tsaron kasa mai fadi kamar Najeriya daga Abuja ba.” Haka Osinbajo ya furta.
Discussion about this post