Majalisar Tarayya ta hautsine dalilin dala biliyan daya da Buhari zai sayo makamai

0

Zaman Majalisar Wakilai ta Tarayya na jiya Alhamis ya hautsine yayin da aka gabatar da batun neman amincewa ga Shugaba Muhammadu Buhari ya kwashi dala bilyan daya domin a sayo makaman da za a yaki Boko Haram da su.

Hayaniyar ta fara kaurewa ne a lokacin da Dan Malalisar Tarayya daga Jihar Ribas, Ken Chikere ya nemi a cire wa jihohin da ke da arzikin man fetur rarar kashi 13 bisa 100 daga cikin dala bilyan daya da Buhari ya nemi ya dauka ya sawo makamai.

Chikere ya ce idan ba a dibar musu kason su daga cikin kudin ba, to karyar dokar kasa ta 1999. Sashe na 16 (2).
Sai ya yi kira ga Ma’aikatar Harkokin Kudi da ta tabbatar an yankar wa kowace jiha mai arzikin danyen mai kashi 13 bisa 100 da ake ba ta.

Sai dai kuma Hon. Shehu Garba daga jihar Kaduna, ya ce bai kamata a saka bangaranci ko shiyyanci a yaki da Boko Haram ba. Ya kara da cewa kamata ya yi a kalli Boko Haram a matsayin matsala ta kasa baki daya.

Ya ce idan aka ci gaba da kacalcala maganar, to za ta tono abubuwa da yawa da za a iya shigar da siyasa a ciki.

Shi kuwa Hon. Henry Archibong, ya ce ya kamata kada a sake a taba kudin har sai idan Majalisar Tarayya ta amince tukunna.

Sai da kuma Mataimakin Kakakin Majalisa, Yusufu Lasun, ya ce kafin a kalli yawan kudin, kamata ya yi a fara yin nazarin daga inda kudin zai fito tukunna, sannan mutum ya san abin da zai rika babatu a kai.

Ya ce daga aljihun gwamnati kai tsaye za a debi kudaden, ba daga cikin jimillar kudaden da gwamnatin tarayya ke rabawa a duk karshen wata ba.

“Ya kamata mu sani cewa matsalar Boko Haram ta shafi kowa a kasar na, ba matsala ba ce ta bangaren ko yanki daya. Mun gaji da asarar rayuka da cin bakar wahala a kan Boko Haram.”

A nasa jawabin, Kakakin Majalisa Yakubu Dogara ya tunatar da mambobin majalisar cewa wadannan kudade fa daga asusun gwamnonin jihohi za a cire su, kuma su ne suka amince da cira a lokacin da suka yi taro da Shugaban Kasa a Fadar sa.

Kuma ya kara da cewa Majalisun Jihohi sun rigaya sun amince, sun yarda a cire kudaden daga aljihun gwamnatin jihohin su.

Don haka sai Dogara ya ce, shi bai ga abin tada jijiyar wuya da har Majalisar Tarayya za ta tashi hankalin sa kan batun da bai shafe ta ba.

Sai kuma ya nemi da a tabbatar da halin da asusun ke ciki tukunna kafin nan da sati hudu domin majalisar tarayya ta san inda ake ciki.

Share.

game da Author