An kashe hamshakin dan siyasa a Kaduna

0

Wasu makasa da ba a san ko su wane ba, sun kashe Moses Banka, wani babban dan siyasar karkara a Karamar Hukumar Jema’a, jihar Kaduna.

An kashe shi ne a cikin gidan sa da ke kauyen Ankwa, cikin karamar hukumar jema’a.

Kantoman Karamar Hukumar mai suna Yusuf Usman ya tabbatar wa Kamfanin Dillancin Labarai (NAN) aukuwar wannan kisa da ya ci ranar Laraba da tsakar dare aka kashe shi.

Usman ya ce an aika rahoton ga ‘yan sanda su kuma su na ci gaba da kwakkwaran bincike.

Banka dan Anakin Karamar Hukumar Sanga ne, sannan kuma baya ga siyasa, babban manomi ne.

Wani mazaunin garin Gwantu mai suna Yuguda Dauda, ya bayyana cewa ba za a manta da gudummawar da Banka ya yi wa jama’a ba, musamman yadda ya gina hedikwatar karamar hukumar Sanga a garin Gwantu shi kadai kyauta da kudin sa.

Share.

game da Author