Mai martaba sarkin Kano Muhammed Sanusi II ya yi kira ga matan arewa da su yi amfani da baiwar da Allah ya basu wajen samar da hanyoyin da za a iya bi don gyara halayyar mutanen yankin Arewa.
Da yake gabatar da jawabin sa a wajen taron kadamar da wani littafi da uwar gidan gwamnan jihar Kaduna Hadiza El-Rufa’I ta rubuta mai taken ‘Yalwan kunama’ wato ‘An Abundance of Scorpions’ wakilin sarki Ahmad Umar ya ce sarki Sanusi ya kalubalanci matan shugabannin kasar nan da su yi koyi da Hadiza wajen yin amfani da damar da suke dashi domin gyara tarbiyya da dabi’un al’umma.
Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai wanda yana daga cikin manyan baki da suka halarci bukin kaddamar da littafin ya jinjina wa uwar gidan sa saboda hangen nesa da tayi wajen tabbatar da ta wallafa irin wannan littafi.