Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta yi watsi da neman belin da lauyan Maryan Sanda ya nemi kotu ta bayar.
Ana tuhumar Maryam ce da laifin kashe mijin ta, Bilyaminu Bello, da ga tsohon Ministan tsaro, Bello Halliru, sannan kuma tsohon shugaban jam’iyyar PDP na kasa baki daya.
Wannan ne karo na biyu da ta nemi beli amma aka hana ta. A makon da ya gabata lauyan ta Joseph Daudu ya bayyana wa Mai Shari’a cewa Maryam ta na dauke da ciki wata uku, don haka ana neman beli domin a samu yadda za a rika kula da ita, ita kuma ta na kula da jinjirin da ke cikin ta.