Fasinjojin da suka hau jirgin Dana sun sauka sun kerkerma bayan murfin kofar jirgin ya fado a daidai jirgin na kokarin sauka.
Wasu daga cikin Fasinjojin sun fadi cewa abin ya yi matukar tada musu hankali.
” Tunda muka hau jirgin yake gigir-gigir, kamar za-a-ba-za- a ba. Ile ko a daidai zamu sauka sai kofar jirgin ya balle ya fado. Ni na dauka bam ne ma. Allah ya taimaka mun sauka lafiya.” Inji Wani fasinja.
Da muka nemi ji ta bakin jami’an kamfanin Dana din, sun ce ba za su iya cewa komai ba sai sun tattauna da Injiniyoyin su.