Yadda rikicin wasikar Babangida ya ritsa da wakilin PREMIUM TIMES a Hedikwatar ‘Yan Sanda

0

‘Yan sanda a Hedikwatar su ta Abuja, sun tsare wakilin PREMIUM TIMES a tsawon wani dan lokaci, yayin da ya tafi rakiyar Kassim Afegbua zuwa kai kan sa ga jami’an tsaro.

Afegbua, shi ne kakakin yada labaran tsohon shugaban kasa, Ibrahim Babangida, wanda ya fitar da wasikar da Babangida ya yi kiran Shugaba Muhammadu Buhari da ya hakura ya janye kada ya sake tsayawa takara.

Jami’an tsaro na tuhumar sa da cewa ya kirkiri karya ya rubuta, shi kuma ya tsaya tsayin daka cewa da sanin Baban gida aka rubuta takardar.

Daga baya Bababngida ya fito ya ce da sanin sa aka rubuta takardar. Amma duk da haka jami’an tsaro ba su hakura ba, suka ce sai sun kama Afegbua.

A yau Laraba. Afegbua ya kai kan sa hedikwatar ‘yan sanda ta kasa da ke Abuja, tare da lauyan sa, Kayode Ajulo da kuma rakiyar ‘yan jarida hudu masu take masa baya, ciki har da wakilin PREMIUM TIMES Na Musamman, Samuel Ogundipe.

PREMIUM TIMES ta hada wakilin na ta Ogundipe ya bi Kassim Afegbua ya dauko labarin duk yadda ta karke tsakanin sa da ‘yan sanda, kua ya dauki bidiyon shigar Afegbua harabar hedikwatar har shigar sa cikin dakin da ake karbar baki.

Sai dai kuma isar su dakin karbar baki ke da wuya, sai jami’an tsaro su ka kwace wayar Ogundipe, a bisa neman dalilin da ya sa ya dauki hoton bidiyo da wayar a cikin hedikwatar ‘yan sanda ta kasa.

A lokacin da aka karbi wayar Odundipe, ya rigaya ya dauki bidiyon yadda aka tarbi tawagar ta su, da kuma yadda aka karke a lokacin da Afegbua da lauyan sa su da Ogundipe suka shiga a ciki.

Kafin nan dama ba su bar sauran ‘yan jarida uku sun shiga cikin harabar hedikwatar ba, amma shi Ogundife ya shiga tare da Afegbua, kuma ana tafiya ya na daukar hoton bidiyo.

Yayin da su ka isa, sai jami’an tsaro su ka nemi Afegbua ya gabatar da kan sa. A bisa dukkan alamu ba su ma san ko wane ne shi ba, duk kuwa da cewa an buga sanarwar su na neman sa ruwa a jallo. Sun kuma tambayi wa ke neman sa.

Daga nan sai ya shaida musu cewa Mashood Jimoh, kakakin yada labaran ‘yan sanda ya buga sanarwar ana neman sa, ga shi kuma ya kawo kan sa.

Daga nan sai lauyan sa Ajulo ya fusata, ya ce ‘to idan Mashood bai shirya bas u fa za su koma kawai abin su.”

Daga nan kawai sai wasa ya koma sabon lale, inda wasu jami’an tsaro su ka bada umarnin a kwace wayar wakilin PREMIUM TIMES, kuma kada a bar shi ya fita.

Gungun jami’an ‘yan sanda masu yawa fa suka kewaye Ogundipe sun a cewa lallai sai ya goge bidiyon da ya dauka, shi kuma ya na cewa ba zai goge ba, tunda ba su ya ke yi wa aiki ba. Daga cikin wadanda suka zakalkale a kan Ogundipe, har da wani mai suna James Oyibo da kuma Daniel James.

Nan dai aka yi ta karankatakaliya, shi kuma ya na nuna musu cewa dan jarida ne kuma dama shi abin da ya kawo shi kenan.

Ganin ya jajirce ya ki yarda ya goge bidiyon, su kuma su ka ce to ba za su bari ya fita ba. Sai bayan an dauki lokaci kadan sannan aka ce ya tafi, bayan da wata jami’a mace ta shigo ta ce “wannan ai wakilin PREMIUM TIMES ne.”

Da ka tambayi Mashood kana bin da ya faru, ya ce a halin da ake ciki ba zai iya karbo, wayar Samuel ba.

“Dukkan ‘yan jaridar da su ka biyo Afeguba a yau Laraba, ba su sanar da ni cewa za su zo ba. Don haka ni a yanzu ban san abin da zan iya yi ba tukunna.”

Sai dai kua Mosheed ya ce Ogundipe ya yi kuskure da ya dauki hoton bidiyo a cikin harabar ofishin ‘yan sandan.

“Kamata yay i ka ajiye wayar ka a daidai kofar da ake shigowa ka karbi katin shaidar ka ba su ajiyar wayar ka.” Inji Mashood.

Amma kuma ya yi alkawarin zai karbo musu wayar sa ba da dadewa ba. Bayan an yi kamar minti 20 shiru bai ga an maida masa wayar sa ba, sai Ogundipe ya fusata, ya yi fitowar sa ya bar musu wayar.

Bayan ya dawo ofis, an kira wayar Mashood kuma an yi masa text domin a ji inda aka kwana dangane da wayar da ke hannun jami’an su, amma bai amsa kiraba, kuma bai turo sakon text ba.

Share.

game da Author