Dalilin da ya sa na ke fada da Kwankwaso – Ganduje

0

Gwamnan Kano, Umar Ganduje ya bayyana cewa hotunan kananan yara da aka rika yawo da su a soshiyal midiya ana cewa sun yi zabe a Kano, ba gaskiya ba ne, sharrin abokan adawa ne, kuma farfaganda ce.

Da ya ke magana da manema labarai a Fadar Shugaban Kasa, Ganduje ya ce abin duk sharrin farfaganda ce da magoya bayan Rabiu Kwamkwaso su ka kitsa masa.

“Ku tambayi masu sa-ido daga kasashen waje da suka halarci zaben, sun gabatar da taron manema labarai bayan sun zagaya. Amma hotunan kananan yaran nan duk farfaganda ce.”

Ya kuma bayyana cewa Kwankwaso ne ya buge da farfaganda saboda ya kasa zuwa Kano ya shiga zaben.

“Ku tambaye su, shin sun je sun shiga layi sun dangwala kuri’a? Ai ba su iya zuwa ba. Don haka ba mu ma da lokacin da za mu tsaya mu na ja-in-ja da su.”

“Abu mafi muhimmanci shi ne sai ku je ku tambayi wadanda suka bi layi suka jefa kuri’a ku ji abin da za su shaida muku.

Dangane da karankatakaliyar rikicin sa da tsohon ubangidan sa, Sanata Rabi’u Kwankwaso, Ganduje ya ce, sun shafe shekaru masu yawa su na tare.

Ya ci gaba da cewa tarihin siyasar sa ba za ta taba cika ba tare da Kwankwaso ba, kamar yadda ta Kwankwaso ba za ta cika ba tare da Ganduje ba.

Daga nan sai ya ce amma maganar gaskiya ita ce ya na fada da Kwankwaso ne saboda ya ki yarda Kwankwaso ya rika juya shi kamar waina, alhali shi kuma ya yi nasa mulkin ya gama.

“Kun san yadda yanayin mulki ya ke. Bai yiwuwa a ce ka na mulki amma ba kai ke mulkin ba, wani can ne zai rika jujjuya ka daga waje.” Inji Ganduje.

Share.

game da Author