Soyinka ya koka da tafiyar mulkin Buhari

0

Wole Soyinka ya bayyana damuwar sa da irin yadda Shugaba Muhammadu Buhari ke yawan tafka kura-kurai a yanayin tafiyar da mulkin sa.

Ya yi wannan bayani ne yayin da ya ke ganawa da manema labarai, inda ya nuna damuwar sa kan yawan masu rajin neman kare bangaren su da ke yawan bayyana a kasar nan.

Ya ce yawanci masu wannan raji sun bayyana ne sakamakon irin rikice-rikicen da ake samu tsakanin makiyaya da manoma.

Da aka tambaye shi ko me zai iya fada wa Buhari idan har su ka hadu su biyu, sai Soyinya ya ce, “Zan shaida masa cewa, ‘Shugaban Kasa ka fa lula ka na barci mai nauyi, ba ka ma san abin da ke faruwa a kasar nan ba. Kuma ana ta tafka manyan kura-kurai na ba gaira ba dalili.” Inji Soyinka.

Ya kawo dalili daya daga cikin kura-kuran da ya ce ana tafkawa, inda ya buga misali da yadda shugaba Buhari ya maida Shugaban Hukumar Inshorar Lafiya ta Kasa, NHIS, Usman Yusuf, wanda Ministan Lafiya Isaac Adebowale ya dakatar saboda zargin harkalla.

Share.

game da Author