Kakakin hukumar hana yaduwar cutar Kanjamau na kasa NACA Toyin Aderibigbe ya yi kira ga matasa maza da mata da su rika kiyaye saduwa da junan su batare da kariya ba.
Toyin ya ce ya zama dole su rika yin irin wannan tunatarwa ganin cewa a yanzu matasa na fara saduwa ne a tsakanin su tun kafin su kai shekaru 15, cewa idan ba ayi haka ba za a iya fadawa matsala.
Ya kara da cewa bincike ya nuna cewa kashi 4.2 bisa 100 na matasan Najeriya masu shekaru 15 zuwa 24 sun fi kamuwa da cutar kanjamau sannan kashi 17 bisa 100 ne kawai suka san matsayin su game da cutar kanjamau .
” Yin wannan kira ta zama dole musamman yadda muka shiga wannan makon masoya.”
Aderibigbe ya ce cutar kanjamu na kara yaduwa tsakanin matasa a kasar nan saboda rashin kare kan su lokacin da za su sadu da juna, inda wasu kuma ma da yawa ba su tsaya ga mutum daya ba.
” Yayin da muka shiga wannan mako na masoya ina kira a gare ku da ku yi amfani da wannan dama wajen kare kan ku daga kamuwa da cutuka da akan kama ta hanyar jima’i sanan da kare kai daga daukar cikin da ba’a so.”
Daga karshe ya kuma yi kira ga masoya da su yi amfani da wannan rana don sanin matsayin su game da cutar Kanjamau domin babu sauran more rayuwa idan har dai mutum ya bari cutar kanjamau ta kama shi ba tare ya sani ba.
Discussion about this post