BATA SUNA: El-Rufai ya maka Shehu Sani a kotu

0

Gwamnan Jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya shigar da Kara a kotu dake Kaduna yana neman ta hukunta sanata mai wakiltan Kaduna ta tsakiya Shehu Sani saboda bata masa suna sannan ta tursasa shi ya biya shi naira biliyan 2 dalilin haka.

Jarida Punch ne ta ruwaito wannan labari inda ta ce Shehu Sani ya kira gwamna El-Rufai bugagge, sannan shi na abin alfahari bane ga shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Lauyan El-Rufai ya Abdulhakeem Mustapha ya bayyana wa manema labarai bayan ya shigar da karar a harabar kotun cewa ya zama dole El-Rufai ya shigar da kara ganin cewa cin fuskar ta yi yawa.

Muna tuhumar sa da yi mana kazafi, cin fuska, karya da tonon silili kuma a kowani daya muna neman ya biya mu naira miliyan 500.

Share.

game da Author