Kungiyar dattawan arewa NEF ta nada sabbin shugabanin da zasu ci gaba da gudanar da aiyukan Kungiyar.
Shugaban kwamitin da Kungiyar ta kafa Mohammed Kirfi ne ya bayyana haka ranar Laraba a Abuja.
Cikin wadanda aka nada sun hada da Ango Abdullahi sabon shugaban kungiyar, Sani Zangon- Daura, mataimakin shugaban kungiyar na yankin Arewa maso gabas, Yahaya Kwande mataimakin shugaban kungiyar yankin Arewa ta tsakiya.
Kungiyar ta kuma nada mambobin kwamitin amintattu 21 da mambobin kwamitin gudanarwa na kungiyar.
Discussion about this post