Matar shugaban kungiyar taratsin gwagwarmayar neman kafa kasar Biafra, Nnamdi Kanu, ta bayyana cewa bacewar da mijin ta ya yi aka daina ganin sa, shi ne babban abin da zai iya sauya akalar yiwuwa ko rashin yiwuwar zaben 2019, idan lokacin zaben ya zo.
Uchechi Kanu, ta yi wannan jawabi ne a lokacin da ta ke zantawa da BBC a yau Litinin, ta kara da cewa idan gwamnatin Nijeriya ba ta bayyana inda Kanu ya ke ba, to ba za a yi zaben 2019 ba.
“Idan lokacin zaben ya zo, maganar Nnamdi Kanu ita ce a kan gaba. Da farko ma dai tukunna, ya na ina ne? Mu na bukatar ku fito mana da shi, ko domin mu ma san inda ya ke. Ya kamata ku fa yi wani abu kafin ma ku zo ku ce za ku gudanar da zabe. Idan bah aka ba kuwa, to ba za mu iya fita mu yi zaben ba.”
Kanu dai a zaman yanzu, hukumar tsaron sojoji na neman sa ruwa a jallo, rabon da a gan shi tun ranar 27 Ga Satumba, 2017, lokacin da sojoji su ka kai farmaki gidan sa a jihar Abia.
Amma sojojin sun musanta zargin da wasu ke yi cewa Kanu ya na hannun su a tsare.
Matar ta sa ta kara jaddada cewa tilas sojoji su fito su bayyana wa duniya inda Kanu ya ke, saboda har yau daga cikin iyalin sa ko dangin sa, babu wanda ya san inda ya ke, balle ma labarin sa. Ko a raye ko ya na mace, duk ba su sani ba.