Kungiyar Kare ‘Yancin Musulmai ta Najeriya, MURIC, ta bayyana cewa wadanda su ka wawure dukiyar kasar nan, maciya hanci da rashawa su ne ke ta caccakar Shugaba Muhammadu Buhari, wanda kungiyar ta kira ” nagari na kowa banda mugu.”
MURIC ta buga misali da yadda shugaban Afrika Jacob Zuma ya yi murabus bayan an zarfe shi da laifin cin rashawa.
Kungiyar ta ce amma abin mamaki a kasar nan, sai Buhari ake ta caccaka saboda yadda ya ke yaki da cin hanci da rashawa.
Sakataren Kungiyar MURIC, Ishaq Akintola ne ya bayyana haka, ya na mai cewa a yau Najeriya ta zama abin dariya a idon kasashen duniya, ganin yadda tsoffin shugabannin kasar nan biyu da kuma majalisar tarayya ke ta kokarin ganin wai Shugaba Muhammadu bai sake tsayawa takarar shugabancin kasar nan a 2019 ba.
“Saukar Jacob Zuma na Afrika ta Kudu daga mulki abu ne mai koyar da darasi.
A waje daya an ga yadda kasar Afrika ta Kudu ba ta amince da shugaba mai wawurar kudi ba, a gefe daya kuma a nan Najeriya, shugaban da ke yaki da masu wawurar kudin shi ne ba a so ya ci gaba da mulki.
Akintola ya ci gaba da bayyana irin nasarorin da Buhari ya kawo, musamman wajen toshe kofofin da baragurbin ‘yan Najeriya ke wwurar kudade da kuma inganta harkokin noma da sauran su.
Daraktan na MURIC, ya ja kunnen ‘yan Najeriya cewa su yi kaffa-kaffa da wadanda suka sace kudin Najeriya, yanzu kuma su ka dawo su na sukar Buhari da nufin rage masa farin jini.
Ya ce zargin da ake yi masa na kabilanci da fifita wani yanki ko shiyya, duk farfaganda ce, wadda ba za ta yi tasiri ba.