Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa dukkan kadarorin da aka sace, amma har yau bayan an kwato, babu wanda ya zo ya ce na sa ne, to za a sayar da su.
Kadarorin da Buhari ke magana sun hada da kayayyaki da filaye da gidaje da sauran su. Ya yi wannan jawabin ne a ranar Litinin a lokacin da ya ke wa Kungiyar Masarautar Daura jawabi lokacin da suka kai masa ziyara a gidan sa na Daura, jihar Katsina.
Buhari ya ce akwai tulin kadarorin da gwamnatin tarayya ta kwato daga hannun barayin gwamnati da dama a cikin kasar nan.
“Wasu shekaru can baya da su ka wuce, wani da mu ka yi makaranta tare da shi, da ya yi aiki a wani kamfani, ya taba ce min, Allah zai kawo lokacin da a kasar nan wata rana za ta zo da mutum zai saci dukiyar gwamnati amma a bi shi a kwato wa jama’a kayan su.
“Idan ka na ma’aikacin gwamnati, amma sai aka same ka da gidaje kamar goma a Abuja, har da Kaduna da kasashen waje, ina ka same su? A yanzu da zaran ka nuna musu ka ce wadannan gidajen ka ne, sai su yi ta zabga rantsuwa su na cewa wallahi ba na su ba ne.
“To mu na nan dai mu na bin abin daki-daki, kun san ita dimokradiyya sai ana bi sannu.
“Idan ku na bin abin da ke faruwa, za ku rika jin wasu da suka saci dukiyar ana kama su, to su kuma wadanda aka kwace ta su dukiyar da suka sata, da wadanda aka nuna musu na su kantama-kantaman gidajen amma su ka ce ba na su ba ne, duk za mu sayar da su, a zuba kudin a asusun gwamnatin tarayya.”
Discussion about this post