TUKIN GANGANCI: Yaron da ya kashe mutane a Gusau, ya gudu

0

Wani karamin yaron da ya tuka mota a cikin Gusau, babban birnin jihar Zamfara, ya gudu bayan ya banke mutane uku sun mutu.

Rahotannin da Kamfanin Dillancin Labarai ya tabbatar sun nuna cewa hadarin ya auku ne sanadiyyar tukin gangancin da yaron ya yi.

Kakakin Yada Labaran ’Yan sandar jihar, Mohammed Shehu, ya bayyana cewa ana nan ana binciken lamarin.

Hadarin ya auku ne tun a ranar Litinin, yayin da kuma har yau ba a kamo yaron ba. Amma kuma jamai’an tsaro sun ce sun a da cikakkun bayanan yaron.

Shi ma Jami’in Hulda da Jama’a na Jami’an Hukumar Kar Hadurra ta Kasa, FRSC, Nasir Ahmad, ya ce hukumar su ta samu rahoton wannan mummunar hadarin ganganci da ya auku.

“Mu ma mun samu labarin, amma ‘yan sanda sun dauke gawarwakin wadanda hadarin ya ritsa da su. Don haka maganar yanzu ta na a hannun su ‘yan sandan kenan.

Wani da aka yi hadarin a kan idon sa, ya nemi a sakaya sunan sa. Amma ya ce yaron da ke tuka motar kirar Marsandi, ya saki motar ce a sukwane, kuma a kan titin da ke da dandazon jama’a da ababen hawa.

Amma kuma ya tabbatar da cewa motar kwace masa ta yi, ta rufta cikin jama’a.

Daya daga cikin mamatan da aka banke, daliba ce da ke karatu a shekarar karshe a Makarantar Koyon Aikin Jiyya da Ungowarzoma.

Share.

game da Author