NDLEA ta kama wata mota dankare da tabar wiwi ‘SKUNK’ a Adamawa

0

Hukumar yaki da hana sha da safarar miyagun kwayoyi ta kasa ‘NDLEA’ ta kama wata motar kirar bas dankare da kilo gram 25.6 da tabar wiwi wanda ake kira da ‘Cannabis Skunk’ a Yola jihar Adamawa.

Shugaban hukumar NDLEA reshen jihar Adamawa Yakubu Kibo ne sanar da haka wa manema labarai a Yola. Kibo ya kara da cewa sun kama mutane hudu wandanda ake zargi suke da mallakin wannan tabar wiwin da aka kama a hanyar Yola zuwa Numan ranar 19 ga watan Janairu.

” Cannabis Skunk wata irin tabar wiwi ce wanda ake shigowa da ita kasar nan daga kasashen waje wanda ta fi tabar wiwi yin illa.”

” A yanzu haka wasu mata na nan tsare a wurin mu dalilin kama su da mukayi suna siyar da irin wannan tabar wiw mia suna Skunk.”

Daga karshe ya yi kira ga direbobin motocin haya da su guji bada motocin su haya batare da sanin abin da suke dauka ba.

Ya ce za su kwace motar sannan su kulle duk wanda suka kama yana aikata haka na tsawon lokaci.

Share.

game da Author