HAJJI 2018: Adamawa tayi kira ga maniyyata da su hanzarta biyan kudin Hajji

0

Hukumar kula da jin dadin Alhazai na jihar Adamawa SPWB ta yi kira ga maniyyata aikin hajjin 2018 da su hanzarta biyan kudaden kujerun su kafin lokaci ya kure.

Shugaban hukumar Umar Babboyi ne ya yi wannan kira yau Laraba, sannan ya fadi cewa daga cikin kujeru 2,601 da jihar ta samu kashi 20 bisa 100 ne kawai suka kammala biyan kudin kujerun su sannan hukumar za ta daina karban kudaden maniyyatan ne a watan Maris 2018.

” Saboda haka ne ya sa muke kira ga maniyyata da su hanzarta biyan kudaden kujeru su domin kasar Saudi ta sami damar kammala shirye shiryen da take yi.”

Daga karshe ya ce duk da cewa hukumar bata tsayar da wata takamammen farashin kujera ba amma maniyyata za su iya biyan kujeran hajji da farashin da aka biya bara Wato Naira 1.5 kenan. Sannan wadanda suka yi aikin hajji fiye da sau biyu za su biya karin Riyal 2000 wato Naira 165,000 kenan akan kudin kujeran da suka biya.

Share.

game da Author