Kotu ta raba auren wani magidanci saboda matar sa ta cika haihuwa

0

Kotun dake Igando jihar Legas ta warware auren Michael Ayinde da matarsa Glory saboda yawan hahuwar da Glory ke yi.

Michael dan shekara 39 ya sanar wa kotu cewa kafin suyi aure sun yi wa juna alkawarin ‘ya’ya biyu ne kawai za su haifa amma sai gashi ta zauna sai sake ‘ya’ya take ba kakkautawa.

Ya ce dalilin haka kuwa shine don ya sami damar iya basu kula yadda ya kamata. “Sai ga shi yanzu ya’yan mu shida cikin shekaru tara da aure.

Ya ce duk da cewa ya tilasta wa matar sa kan yin amfani dabarun bada tazaran haihuwa amma ta faki idona ta koma asibiti ta sa aka cire mata wanda muka amince tayi.

Sakamakon haka Michael ya ce yana bukatan kotu da warware auren sa da Glory domin ba shi da yanda zai iya kula da ‘ya’ya shida.

“Domin in biyan bukatun iyalai na, na siyar da motoci na biyu sannan ita kuma matata an kore ta aiki saboda yawan daukan hutun haihuwa da take yi.”

Bayan haka alkalin kotun Akin Akinniyi ya yanke hukuncin raba aure saboda Glory ta ki zuwa kotu.

Alkalin ya ce daga yanzu kowanen su na da damar zuwa duk inda yake so batare da wani takura ba.

Share.

game da Author