Shugaban kungiyar sarrafa magunguna ta Najeriya ‘PSN’ reshen Abuja, Jelili Kilani ya gargadi mutane da su rage yawan shan kwayar magani da ake kira ‘Paracetamol’ ko ‘Panadol’ cewa yana yi wa huhu da kodan mutum mummunar lahani.
Kilani ya bayyana haka ne da yake zantawa da kamfani dillancin labaran Najeriya ta yi hira da shi a Abuja.
” Misali hadiyar kwayoyin ‘Panadol’ uku zuwa hudu da wasu kan yi musamman don kau da gajiya kan illata huhu da kodar mutum. Sannan kuma mutum ba zai san illar da maganin tayi masa ba sai ya dau wani lokaci da dama tukuna.”
Ya ce kuma ce illar da maganin ke yi a jikin mutum ba a iya gane shi da wuri sai bayan an yi shekaru da dama.
Ya ce kamata ya yi a shan wannan magani kamar yadda likita ya fada sannan wa cutar da ta kamata.
Daga karshe Kilani y ace idan har dai an sha ‘Panadol’ sau daya kuma ba a sami sauki ba kamata ya yi a tuntubi likita domin samun tabacin cutar dake damun mutum.