SHEKAU YA SAKE BAYYANA: Ya ce iyayen daliban Chibok surukan ’yan Boko Haram ne

0

Shugaban Kungiyar Boko Haram, Abubakar Shekau, ya sake bayyana a cikin wani bidiyo, inda ya yi dogon jawabi, a ciki har ya ke wa iyayen ’yan matan Chibok barkwanci, ya na cewa ai su yanzu surukan su ne, domin sun auri ‘ya’yan su.

A zaman yanzu dai akwai akalla ‘yan matan Chibok 100 a hannun Boko Haram da ke hannun su tun cikin 2014, sai kuma wasu jami’an ‘yan sanda mata su 10 da suka gudu da su a cikin shekarar da ta gabata.

Sabon bidiyon da Shekau ya fitar ranar Litinin da ta gabata, ya nuna wasu mata fiye da dozin daya wadanda suka bayyana cewa dukkan su daliban Chibok ne da aka gudu da su.

Da yawa daga cikin matan su na dauke da jinjirai, alamar da ke nuna cewa mambobin Boko Haram sun aure su kenan, ba tare da umarnin iyayen su ba.

Wata matashiyar yarinya da ta yi jawabi a madadin sauran matan, ta bayyana cewa ana ba su kyakkyawar kulawa a hannun Boko Haram, sannan kuma ba su da niyyar komawa a hannun iyayen su. Sai dai kuma mai maganar ta na sanye da nikab, ba a iya tantance ko wace ce, domin fuskar ta a rufe ta ke.

Wannan sabon bidiyo na Shekau, ya bayyana ne mako daya bayan hukumar tsaron kasar nan ta bayyana cewa ta kakkabe Boko Haram, shi kan sa Shekau shugaban na su, ya na fama cikin matsanancin ciwo da jin jiki. Sojoji sun ci gaba da cewa “Shekau ya zama kwantakwaloson gurgun doki.”

To sai dai kuma idan ba a manta ba, kwanaki uku bayan da mahukuntan tsaro na sojojin Najeriya su ka bayyana cewa sun gama da Boko Haram, sai Majalisar Dunkin Duniya ta bayyana cewa batun gaskiya har yau ba a gama da Boko Haram ba.

Mataimakiyar shugaban majalisar ce, Amina Mohammed, wadda ‘yar Najeriya ce, kuma kafin a zabe ta ta tafi majalisar, ita ce Ministar Muhalli ta gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari, ta yi wannan bayani ne a wata ziyara ta kwana biyu ta gani da ido da ta kai a jihar Borno.

Shi kuwa Shekau, ya rika yi wa iyayen daliban Chibok barkwanci, ya na cewa su karbe su a matsayin surukan su kawai, domin ‘ya’yan su na nan tare da su kuma su na zaune lafiya.

Bidiyon da na dauke da mintina 365, inda a ciki Shekau ya ci gaba da cewa an dauki bidiyon ne ranar Lahadi, 14 Ga Janairu, domin kawai ya karyata rundunar sojojin Najeriya da ke cewa wai ciwo ya kusa kai shi gargara, kuma wai ya zama “kwantakwaloson doki.”

Da ya ke magana kan matan Chibok 107 da ya ce sun samun ‘yancin su a shekarar da ta gabata, ya ce Boko Haram ta bayar da su ne saboda sun ki shiga musulunci, kuma sun ki yarda a aure su.

Sai dai kuma ya ce har yanzu ya na rike da jami’an ‘yan sanda mata su 10 da suka yi awon gaba da su a kan hanyar Damboa zuwa Maiduguri, a lokacin da suka yi wa wata kwambar sojoi kwanton bauna cikin 2017.

Shekau, wanda akasarin maganar da ya yi duk da Hausa ya yi ta, ya ce kokarin da sojoji suka yi na baya-bayan nan da suka kai masa hari domin su kwato jami’an ‘yan sandan, bai yi nasara ba, domin sun gamu da tirjiyar dakarun Boko Haram. Ya kuma yi ikirarin cewa sojoji sun yi asarar helikwafta, tankar yaki, motar daukar dakaru da kuma wasu motoci.

Daga karshe Shekau ya nuno wadannan jami’an ‘yan sanda mata su goma, dukkan su suna kuka.

Share.

game da Author