KADUNA: Firgita da ganin dubban jami’an tsaro ya sa wata mata ta bankade wani dan sanda da mota

0

Wata mata da mota ya kwace wa ta tarwatsa dandazon jami’an tsaro da ke kokarin hana kungiyar kwadago gudanar da zanga-zanga a jihar Kaduna.

Matan mai suna Ummul Khairi wanda ma’aikaciyyar gidan talabijin din NTA ne ta fada wa dandazon jami’an tsaro daidai ta shawo kwanar gab da ofishin NTA da ke kusa da ofishin kwadago na jihar.

Ita dai direban motar Hajiya Ummul Khairi wace ke jan Fijo 307 ta ce jami’an tsaron da ta gani ne ya rikitata.

” Rudewa na yi a lokacin da naga dandazon jami’an tsaro kwawai sai motar ta kwace.”

Wadanda abin ya faru kan idon su sun ce da motar ta kasa shiga kwanar gidan jaridar NTA sai ta nufo inda taron jam’an tsaron suke, kuma motar ta ruguza daya daga cikin motar jami’an tsaron sannan ta daki motar wani ma’aikacin jaridar ‘Leadership’ sannan ta banke wani dan sanda.

Share.

game da Author