Mai Shari’a Mairo Nasir da ke Babbar Kotun Abuja, ta bayar da belin Maimuna Aliyu a kan kudi naira miliyan 10.
Maimuna, wadda ita ce tsohuwar Shugabar Aso Savings and Loan, plc, ana zargin ta ne da wuru-wurun naira miliyan 57 a lokacin da ta ke aiki tare da hukumar Aso Savings.
Idan ba a manta ba, ita dai ce a wata kotun kuma ta ke fuskantar tuhuma dangane da zargin da ake yi wa ‘yar ta Maryam Sanda da kashe mijin ta, Bilyaminu Halliru.
Mai Shari’a Mairo ta bayar da belin ta bayan da lauyan ta, Joe-Kyari Gadzama ya nemi a bada belin na ta.
An kuma nemi mutane biyu da su tsaya mata, wadanda tilas su kasance mazaunan Abuja ne, kuma dole su je kotun su yi rantsuwar iyar gaskiyar aiki ko sana’ar da su ke yi su na samun kudi.
An dage shari’ar sai ranar 12 Ga Maris, 2019 domin a fara sauraren ba’asin karar.