Dan Majalisar Tarayya daga Kaduna ya fice daga APC

0

Shugaban Kwamitin Majalisar Wakilai kan Harkokin Cikin Gida, Adams Jagaba, ya fice daga jam’iyyar APC, ya na mai cewa jam’iyyar ta saki layi, ta koma hauragiya.

Jagaba, shi ne Dan majalisar Tarayya mai wakiltar Kananan Hukumomin Kachia da Kagarko, ya bayyana haka ne jiya Litinin a matsayin martanin da ya bayar bayan jam’iyyar APC reshen jihar Kaduna ta dakatar da shi.

” Jam’iyyar APC ta zama kwale-kwalen da ke tangal-tangal a cikin ruwa. Ni dai ba zan tsaya har ya nutse da ni a ciki ba.”

Duk da dai har yau bai bayyana jam’iyyar da zai koma ba, amma wata majiya ta tabbatar wa PREMIUM TIMES cewa Jagaba zai yi gaba ne zuwa jam’iyyar PDP.

Share.

game da Author