El-Rufai ya nada sabbin Shugabannin ma’aikatu 3

0

Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufa’I ya nada wasu sabin shgabanin ma’aikatu uku a jihar.

Mai taimkamasa kan yada labarai Samuel Aruwan ya sanar da haka a inda ya kara da cewa El-Rufa’i ya nada Sani Abbas mukamin shugaban ‘Kaduna State Mortgage and Foreclosure Authority’.

Ya ce kafin gwamnan ya nada shi wannan matsayin Abbas ya rike mukamin babban darektan na ‘State Industrialisation and Micro Credit Management Board’.

An nada Ben Kure shugaban hukumar bada agajin gaggawa na jihar Kaduna.

Kafin a nada shi wannan matsayin Kure ya rike mukamin shugaban rikon kwarya na karamar hukumar Jaba sannan shine darektan kamfen din jam’iyyyar APC a 2015.

Na karshe kuma shine Musa Usman wanda gwaman ya nada a mukamin babban darekta hukumar‘Kaduna State Facility Management Agency’

Share.

game da Author